1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alpha Conde ya lashe zaben kasar Guinea

Salissou BoukariOctober 18, 2015

Hukumar zaben kasar Guinea ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar wanda ya baiwa Shugaba Alpha Konde nasara da fiye kashi 57 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada.

https://p.dw.com/p/1GptR
Alpha Conde
Alpha CondeHoto: picture-alliance/AP Photo/R. de la Mauviniere

Sanarwar hukumar zaben kasar ta Guinea ta ce madugun 'yan adawar kasar Cellou Dalein Diallo na a matsayin na biyu da kashi 31, 5 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada.Tuni dai madugun 'yan adawar kasar, ya yi kira ga sauran 'yan takara da ma al'ummar kasar ga wata zanga-zanga ta lumana domin nuna bakin cikinsu da abun da suka kira kwace.

'Yan adawar kasar ta Guinea dai sun zargi bangaren shugaban mai ci da tafka magudi, ta hanyar yin aringizon kuri'u a wasu yankuna, da baiwa kananan yara damar yin zaben, da kuma amfani da jami'an tsaro don baiwa wakillan 'yan adawar tsoro. A halin yanzu dai 'yan takarar na da kwanaki takwas na kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotun tsarin mulkin kasar.