Almundahana a shirin sayar da man Iraki don saye mata abinci | Labarai | DW | 28.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Almundahana a shirin sayar da man Iraki don saye mata abinci

Wani kwamitin binciken MDD ya ce sama da kamfanoni 2200 daga kasashe 66 ke da hannu a zargin cin hanci da rashawa da ya shafi shirin sayar da man Iraqi a saye mata abinci da magunguna. Rahoton karshe da kwamitin binciken karkashin jagorancin tsohon shugaban babban bankin Amirka Paul Volcker ya bayar ya ce kamfanonin sun ba gwamnatin tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein toshiyar baki ta kimanin dala miliyan dubu 1.8. Kamfanoni kamar su Daimler-Chrysler da Siememns na daga cikin jerin kamfanonin da rahoton ya ce sun ba jami´an tsohuwar gwamnatin Iraqi hanci don samun kwangila daga gwamnatin birnin Bagadaza.