Allah Ya yiwa sarkin Kuwaiti Sheikh Jaber al-Ahmed al-Sabah rasuwa | Labarai | DW | 15.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Allah Ya yiwa sarkin Kuwaiti Sheikh Jaber al-Ahmed al-Sabah rasuwa

Gidan telebijin Kuwaiti ya ba da sanarwar rasuwar sarkin kasar Sheikh Jaber al-Ahmed al-Sabah bayan yayi fama da zubar jini a kwakwalwarsa shekaru 5 da suka wuce. Yanzu haka dai wani dan´uwansa na nesa da sarkin ya nada zai gaje shi. Shine Sheikh Saad al-Abdullah al-Sabah. Tun a cikin shekarar 1977 marigayi sarki Jaber al-Ahmed ke shugabantar kasar ta Kuwaiti, daya daga cikin manyan kawayen Amirka a yankin GTT. A 1990 sarkin ya tsere zuwa Saudiyya bayan da Iraqi ta mamaye Kuwaiti. Shi ya shirya bijirewa wannan mamaya sannan bayan yakin Gulf a 1991 ya koma gida Kuwaiti. Yanzu haka dai gwamnati ta bayyana zaman makoki na kwanaki 40.