1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Allah ya yi wa Winnie Mandela rasuwa

Salissou Boukari
April 2, 2018

Rahotanni daga kasar Afrika ta Kudu na cewa, Allah ya yi wa Winnie Mandela wadda take tsohuwar mai dakin tsohon shugaban kasa, Nelson Mandela, rasuwa.

https://p.dw.com/p/2vNUB
Südafrika Winnie Mandela
Marigayiya Winnie Mandela Hoto: Imago

Winnie Mandela mai shekaru 81 ta rasu ne a wannan Litinin a babban asibitin Milkpark da ke birnin Johannesburg, kamar yadda mai magana da yawunta Victor Dlamini ya sanar, inda ya ce ta rasu ne bayan ta yi fama da dogon rashin lafiya.

Winnie Madikizela ta yi aure da Nelson Mandela ne tun a shekara ta 1958.

Ana yi wa marigayiyar kallon daya daga cikin shika-shikan yaki da wariyar launin fata a kasar ta Afrika ta Kudu, wadda ake ganin ta sadaukar da rayuwarta wajen samarwa da kasarta 'yanci.

Sai dai kuma a hannu daya yanayi da take da shi na tsauraran ra'ayi da ma zargin masu bata kariya da laifin kisan kai, ya sanya tazara tsakaninta da maigidanta marigayi Nelson Mandela, inda suka rabu a shekarar 1996 shekaru biyu bayan da Mandela ya hau kan karagar mulkin kasar ta Afrika ta Kudu.