Allah Ya yi wa mashahurin mawakin kasar Kwango, Papa Wemba rasuwa | Labarai | DW | 24.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Allah Ya yi wa mashahurin mawakin kasar Kwango, Papa Wemba rasuwa

Papa Wemba wanda ake yi wa kallon sarkin salon kidan "Rumba" ya rasu yana da shekaru 67. Ya gamu da ajalinsa ne lokacin wani bikin kade-kade a kasar Cote d'Ivoire.

Wani daga cikin manyan jami'an kula da dakin gawa inda aka aje gawar Papa Wemba din ya ce mawakin ya yanke jiki ya fadi ne a daidai lokacin da yake gabatar da waka a wani biki na musamman na kida da rawa da aka shirya. Kuma Allah Ya karbi ransa a kan hanyar kaishi asibiti.

Mawakin dan shekaru 67 a duniya da kuma ake bayyana shi a matsayin sarki a fannin salon kidan "Rumba" da ma iya sanya tufafi, yana da tarin masoya a kusan duk fadin nahiyar Afirka da ma Turai. Dan asalin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ne amma ya koma birnin Paris na kasar Faransa da zama.

Wannan rasuwa ta Papa Wemba ta zo ne kwanaki uku bayan da Allah Ya yi wa Prince shi ma wani shahararren mawaki dan Amirka wanda ya yi fice a salon kidan Pop ko Funky rasuwa.