1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alkawarin taimakon kudi ga kasashen Asiya

January 4, 2005

Sakatare-janar na MDD Kofi Annan na tababa a game da cika alkawururrukan da kasashe suka yi na ba da taimakon da ya kai dalar Amurka miliyan dubu biyu ga kasashen Asiya

https://p.dw.com/p/Bvdq
Sakatare-janar na MDD Kofi Annan
Sakatare-janar na MDD Kofi AnnanHoto: AP

An dai saurara daga bakin sakatare-janar na MDD Kofi Annan yana mai fadin cewar kimanin dalar Amurka miliyan dubu biyu ne gwamnatocin kasashe da kuma bakin duniya suka yi alkawarin bayarwa, amma fa mai yiwuwa a karshe a wayi gari adadin kudaden taimakon ya gaza haka. Amma duk da haka, a wannan karon Kofi Annan ya bayyana kwarin guiwarsa fiye da yadda lamarin ya kasance a tarurrukan da suka gabata na kasashen dake ba da lamuni, inda aka saba gabatar da alkawururruka ba tare da an cika su ba. Ya kuwa bayyana dalilin haka yana mai cewar:

Su kansu kasashen yankin sun tashi haikan wajen taimakon kansu da kansu. Kasashen Asiya ba sa fama da gibin albarkatu kuma zan gana da dukkan shuagabannin kasashen a wawware a lokacin taron Jakarta. A sabili da haka nake kyautata zaton cewar akwai kyakkyawan haske a game da cika da yawa daga cikin alkawururrukan da aka yi.

Ita dai MDD ba ta manta da bala’in gizgizar kasar da ya rutsa da garin Bam na kasar Iran shekarar da ta wuce ba, inda kawo yanzu aka kasa cika alkawururrukan taimakon da kasashe suka yi domin sake gina yankin. A wani bayani da yayi Jan Egeland, mai hada kan matakan taimakon jinkai na MDD yayi nuni da cewar a wannan karon azamar taimakon ta zarce ta zamunan baya, inda aka samu kasashe kamarsu Nepal da Timor da wasu kasashe matasa ‚yan rabbana ka wadata mu, wadanda suka bayyana shirinsu na taimako. Kasashen Indiya da China ma, a halin yanzu haka, sune akan gaba wajen ba da taimakon. Kazalika an samu daidaikun mutane masu zaman kansu dake gabatar da taimako, inda misali a kasar Norway kusan kowane daga cikin al’umar kasar ya ba da taimakon dalar Amurka goma. Har yau dai ana ci gaba da tono gawawwakin mutanen da bala’in ya rutsa da su, amma muhimmin abin da ake bukata kamar yadda aka ji daga bakin Jan Egeland, shi ne nagartattun matakai na sake ginawa ta yadda yankunan da lamarin ya shafa zasu samu kafar sake tsayawa kan kafafuwansu. Ya ce masunta ba sa bukatar taimakon kifi sai dai abubuwan da zasu taimaka musu su koma bakin aikinsu. Jami’in taimakon na MDD ya kara da sake janyo hankalin duniya zuwa ga nahiyar Afurka, wadda ya ce akwai sassa dabam-dabam na wannan nahiya cikin hali na kaka-nika-yi, kuma bai kamata hada-hadar taimakon ga kasashen Asiya da bala’in ambaliyar teku ta rutsa da su, ta sanya a sa kafa a yi fatali da makomar kasashen na Afurka ba.