Alkali a shari´ar da ake yiwa Saddam Hussein zai yi murabus | Labarai | DW | 14.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alkali a shari´ar da ake yiwa Saddam Hussein zai yi murabus

Babban alkali a shari´ar da ake yiwa tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein ya mika takardun yin murabus. Kafofin yada labaru sun rawaito cewar alkali Rizgar Mohammed Amin ya fusata dangane da korafe korafen da gwamnatin Iraqi ta yi cewar ya na yiwa Saddam Hussein sassauci. Kawo yanzu dai ba´a sani ba ko an amince da murabus din. Rahotannin da ke iso mana na nuni da cewa jami´an kotun na kokarin sun shawo kan alkali Rizgar da ya ci-gaba da shugabantar zaman sauraron shari´ar. Shari´ar ta tsohon shugaban na Iraqi dai na fuskantar tashe tashen hankula wanda suka yi sanadiyar halaka lauyoyi biyu kawo yanzu. Tun ba yau ba lauyoyin kungiyoyin kare hakkin bil Adam na kasa da kasa ke yin kira ga jami´an Amirka da sabuwar gwamnatin Iraqi da su mika Saddam da mukarrabansa ga wata kotun duniya a ketare.