Alikoftan sojin Birtaniya ya fadi a birnin Basra, akalla mutum biyu sun rasu | Labarai | DW | 06.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alikoftan sojin Birtaniya ya fadi a birnin Basra, akalla mutum biyu sun rasu

Akalla sojojin Birtaniya biyu sun rasu lokacin da wani jirgin saman mai saukar ungulu mallakin rundunar kasar yayi hadari a birnin Basra dake kudancin Iraqi. Wani wakilin kamfanin dillancin labarun AFP da ya shaida hadarin, ya ce ya ga gawawwakin sojojin sun kone kurmus kuma alikoftan yakin na nan yana ta cin wuta. Da farko wani kakakin rundunar sojin Birtaniya ya tabbatar da aukuwar hadarin. Wata sanarwa da ma´aikatar tsaron Birtaniya a birnin London ta bayar ta ce sun samu labarin faduwar alikftan yakin amma ba ta yi karin bayani ba a yanzu saboda ana cikin gudanar da bincike. To amma wani dan sandan Iraqi a birnin Basra ya ce alikoftan ya fado ne bayan an kai masa hari da makami mai linzami a wata unguwa dake tsakiyar birnin. A wani labarin kuma wani dan harin kunar bakin wake ya halaka manyan jami´an tsaron Iraqi 3 a garin Tikrit. Dan kunar bakin wake ya badda kama ne a cikin rigar sarki.