1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ali Larijani na Iran ya ajiye aikin sa ba zato ba tsammani

October 20, 2007
https://p.dw.com/p/Bu86
Babban mai shiga tsakani na Iran a tattaunawar da ake yi dangane da shirinta na nukiliya Ali Larijani yayi murabus. Wani kakakin gwamnati ya ce shugaba Mahmoud Ahmedi-Nejad ya amince da murabus din na Larijani, sannan yanzu haka ana kokarin nada mutumin da zai gaje shi. Shugaba Ahmedi-Nejad ya ce wannan matakin ba zai shafi tattaunawar da ake yi tsakanin kasashen yamma da Iran ba akan shirin ta na nukiliya. Shugaban ya ce magajin Larijani zai gana da babban jami´in diplomasiya KTT Javier Solana a karshen wannan mako kamar yadda aka shirya. Ba´a ba da dalilan murabus din Larijani ba. Kasashen yamma dai na zargin Iran da hankoron kera makaman nukiliya. To amma Teheran ta ce shirin nukiliyar ta na lumana ne.