1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ali Bongo na fuskantar kalubalen kasashen duniya

September 27, 2016

Kungiyar EU da ta Tarrayar Afirka na yin adawa da tabbatar da Ali Bongo da kotun tsarin mulkin kasar ta yi a matsayin shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/2QalA
Ali Bongo Ondimba, neuer Präsident von Gabun
Hoto: AP

Kotun tsarin mulkin kasar ta Gabon ta tabbatar da cewar shugaba Ali Bango ne ya lashe zaben da kashi 50,66% a yayin da abokin hamayyarsa Jean ping ya tashi da kashi 47,24 cikin dari. Sai dai tuni Jean Ping din ya nuna rashin amincewarsa da sakamakon aikin kotun tsarin mulkin kasar ta Gabon yana mai cewar kotun ba ta yi adalci ba.

''Ta hanyar daukar wannan mataki, kotun ta zabi ta kwace wa 'yan kasar Gabon 'yancin da kundin tsarin mulkin kasarsu ya ba su na zabar shugaban kasarsu domin al'ummar Gabon ba  za ta taba fahimtar wanann sakamako ba."

Gabun Opposition Jean Ping Pressekonferenz
Madugun 'yan adawar Gabon Jean Ping ya ce ba za su taba amincewa da sakamakon zaben da ya ba wa Ali Bongo nasaraHoto: Getty Images/AFP/S. Jordan

Tawagar masu sa ido na kungiyar tarayyar Turai ta bakin jagoranta Mara Gabriel ta ce ba ta ji dadi ba da yadda kotun tsarin mulkin kasar ta Gabon ta gaza yin gyaran da yakamata kan kura-kuran da aka tafka a lokacin sake aikin kididdige sakamakon zaben. Musamman dangane da sakamakon zaben  jihar Haut-Ogooue inda aka ce shugaba Ali bango samu kashi 95 cikin dari na kuri'un da aka kada a yankin da a nan ne madugun 'yan adawar kasar ta Gabon ya bukaci da a sake kirga kuri'un. Daga  bangaransa ministan harakokin wajen Faransa Jean Marc Ayrault ya ce aikin da kotun ta yi ya janyo rudani. Ita ma dai kungiyar tarayyar Afirka ta bakin shugabanta Idriss Deby na Chadi  sakamakon aikin da kotun tsarin mulkin ta yi na bukatar sake tatancewa. Shi ma babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon cewa ya yi kawai sun ga sakamakon aikin kotun tsarin mulkin ba tare da  yin wani karin bayyani ba , sai dai ya bukaci mahukuntan  kasar ta Gabon da su saki illahirin mutanen da suke tsare da su ba kan ka'ida ba.