1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alhinin Kenya kan harin Garissa na 2015

'Yan Kenya sun gudanar da bukukuwa da addu'o'i don tunawa da harin ta'addancin da ya hallaka mutane 148 akasarinsu dalibai a jami'ar Garissa a bara.

Dubban 'yan Kenya sun nuna alhininsu a wannan Asabar dangane da zagayowar ranar da tsagerun al-Shabaab suka kai hari a jami'ar Garissa da ke a yankin Arewa maso Gabashin kasar inda suka hallaka mutane 148 akasarinsu dalibai. Sama da mutane 100 sanye da farar riga sun halarci tseren da aka shirya a Garissa da ke da tazarar kilometa 150 daga Nairobi babban birni don karrama wadanda harin ya ritsa da su.

A ranar biyu ga watan Afrilun 2015 ne wasu 'yan bindiga hudu suka kutsa cikin jami'ar inda suka kashe Kiristoci da dama da kuma 'yan sanda uku. Wannan hari ya kasance mafi muni da Kenya ta fuskanta a tarihinta, baya ga wanda aka kaddamar a kan ofishin jakadancin Amirka a Nairobi wanda ya salwantar da rayukan mutane 213.

Aden Duale wanda dan majalisa ne na Garissa ya ce bikin wani nau'i ne na yaki da tsaurin kishin addini, inda ya ce "Mu Musulmin Kenya muna son canja abin da ke faruwa, saboda Musulunci addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna. Wannan abin da suke yi ba shi da dangantaka da addini. Saboda haka za mu dage don ganin mun yaki kaifin kishin addini."