1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahajjata sun fara aikin Hajji

Abdullahi Tanko BalaSeptember 7, 2016

Miliyoyin Alhazai sun hallara a birnin Makkah Domin aikin Hajji

https://p.dw.com/p/1JxGH
Saudi Arabien Mekka Pilger Kaaba
Hoto: picture alliance/AP Photo/skajiyama

Maniyata aikin hajji wadanda yanzu haka suke kasa mai tsarki a Saudiyya, sun hallara a birninn Makkatul Mukarrama a ranar Larabar nan domin fara aikin hajjin bana.

Aikin hajji yana daya daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar da ake bukatar kowane musulmi da ke da koshin lafiya ya gudanar da shi sau daya a rayuwarsa.

Musulmi sun yi imanin aikin hajjin ibada ce da ke tsarkake zukata. Wata daga cikin maniyata daga kasar Morocco Hayat Zangour ta yi bayani tana mai cewar:

" Ta ce Allah mai girma, Allah mai girma wannan shine karon farko da na halarci wannan wuri, na ga Ka'aba kuma ina jin kamar yau na zo duniya".

Daga cikin rukunan Hajjin, mahajjata na gudanar da Dawafi tare da addu'oin neman rahamar Allah subahanahu wata'ala