Alassan watara ya koma gida bayan shekaru 3 na gudun hijira a Faransa | Labarai | DW | 07.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alassan watara ya koma gida bayan shekaru 3 na gudun hijira a Faransa

Bayan shekaru 3 na gudun hujira a kasar Faransa, jiya ne shugaban jami´yar RDR ta Cote D´Ivoire, bugu da kari madugun yan adawar kasar Alassan watara ya koma gida.

Ya samu kyakyawan tarbe daga magoya bayabn sa a filin saukar jiragen sama na birnin Abijan.

Bisa tsartin farko, a wata mai kamawa ne ta kamata Alassan watara ya koma Cote D´Ivoire, ya matso tafiyar jiya, dalili da rashin ma´aifiyar sa.

Ya dawo daga gudun hijirar, kwana daya rak, bayan da shugaban kasa Lauran Bagbo ya sa hannu a kan dokar amincewa, da nada Charles Konnan Banny a matasyin saban Praminsta.

A nasa gefe, shugaban kungiyar tawayen Cote D´Ivoire, Guillaume Soro, ya rubuta wasika zuwa ga komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, inda ya bayyana amincewar kungiyar sa da saban Praministan, saidai ya bukaci Majalisar Dinkin Dunia, ta russa kundin tsarin mulkin kasa, wanda a halin da ake ciki, ya baiwa shugaba Lauran Bagbo, dammar tsige Saban Praministan, inda ya na bukatar hakan.