Alasanne Watara ya ce zai tsaya takarar shugaban kasar Ivory Coast
January 15, 2006Talla
Shugaban babbar jam´iyar adawar kasar Ivory Coast ya ce yana shirin tsayawa takara a zaben shugaban kasar, kuma a shirye ya ke ya koma wannan kasa dake yankin Yammacin Afirka don yiwa jam´iyarsa kamfen. Tsohon FM Allasane Watara ya fadawa jaridar Nord Eclair ta kasar Faranasa cewar lalle zai tsaya takara a karkashin inuwar jam´iyaar RDR. A karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na MDD an shirya gudanar da zaben a Ivory Coast ne a karshen watan oktoban bara, amma aka dage saboda matsaloli na kwance damarun sojin sa kai da kuma na shirya zaben. Kawo yanzu dai ba´a sanya ranar gudanar da zaben ba, amma bisa ga dukkan alamu a ciki wannan shekara za´a yi.