1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alamomin daren lailatul ƙadri

Bashir, AbbaSeptember 29, 2008

Taƙaitaccen bayani game da alamomin daren lailatul ƙadri

https://p.dw.com/p/FN54
Dubban Musulmai na yin ɗawafi a daren azumiHoto: AP

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun mai sauraronmu a yau da kullum Malama Haulatu Ayuba daga Jihar Sokoto a tarayyar Najeriya. Malamar cewa ta yi; Shin ko dagaske ne a daren lailatul-ƙadri ana ganin komai yana yin sujada, kamar bishiyoyi da gidaje, ko kuma mutum yana iya hango ka'aba daga duk inda yake?


Amsa: To dangane da wannan tambaya, mun tuntuɓi Dr. Aminuddeen Abubakar, malamin Addinin Musulunci dake jihar Kanon tarayyar Najeriya, ga kuma abin da ya ce game da amsar wannan tambaya.


Dr. Aminuddeen: A gaskiya irin waɗannan bayanai ba su tabbata daga manzon Allah Sallalllahu alaihi wassamam ba. Kuma magabata na ƙwarai ma ba su tabbatar da haka ba. Faɗin haka ƙoƙari ne kawai na waɗansu mutane ba tare da wani dalili na shari'a ba. Sai dai ya tabbata waɗansu daga cikin sahabbai an nuna musu a mafarki cewa daren lailatul-ƙadri yana cikin bakwan ƙarshe ne. Sai manzon Allah Sallallahu alaihi wasallama ya ce: “Ina ganin mafarkinku ya dace da bakwan ƙarshe, wanda zai nemi daren lailatul-ƙadri to ya neme shi a bakwan ƙarshe.''


Wannan hadisin ya tabbatar da cewa an nuna wa sahabbai ranar da ake sa ran ganin daren lailatul-ƙadri ne, amma ba su ga wani abu bisa saɓanin yadda aka san ɗabi'ar dare ba. Saboda haka zai fi kyau a fahimci daren lailatul-ƙadri a hadisai ingantattu. Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam ya ce; “Ranar da za ta fita bayan daren lailatul-ƙadri, takan fita ne ba tare da zafi ba.''