Alakar Isra′ila da Amurka game da Iraki | Siyasa | DW | 06.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Alakar Isra'ila da Amurka game da Iraki

Wanzuwar sojojin Amurka a Iraki na da muhimmanci ga Isra'ila dangane da manufofinta na tsaro in ji P/M Olmert

P/M Isra'ila Ehud Olmert

P/M Isra'ila Ehud Olmert

Shi dai shugaban gwamnatzin Isra’ila Ehud Olmert na tattare da imanin cewar Amurka ba zata bi wata manufar da zata jefa Isra’ilar cikin mawuyacin hali game da makomar tsaron kanta a yankin gabas ta tsakiya ba. Al’amuran tsaron sun kankama a wannan yankin tun bayan da Amurka ta dirke sojojinta a kasar Iraki, a cewar P/M Ehud Olmert lokacin da yake jawabi ga taron kungiyar Yahudawan Amurka mai suna Orthodox Union. Olmert ya kara da cewar:

“Ina ba da cikakken goyan baya ga shugaba Bush, saboda sikankancewar da na yi cewar kawar da Saddam Hussein daga kasar Iraki abu ne da ya kara kyautata tsaro da kariya ga kasar Isra’ila da sauran kasashen dake makobtaka da ita.”

A ziyarar da Olmert ya kai birnin Washington baya-bayan nan ya samu karin tabbaci daga shugaba Bush a game da cewar babu wani canji na a zo a gani da za a samu a game da manufofin Amurka a YGTT. Shugaban na Amurka ba zai yi masa matsin lamba domin yayi sassauci a dangantaka da Palasdinawa ba. Matsawar da gwamnatin Hamas ta ki ta amince da sharudda guda uku da kasashen yammaci da Isra’ila suka gindaya mata, musamman ma amincewa da hakkin wanzuwar Isra’ila, to kuwa babu wani dalili na shiga shawarwari da Palasdinawa. Bisa sabanin magabacinsa Ariel Sharon, wanda ya ki ya fito fili ya bayyana ribar da Isra’ila ta samu game da al’amuranta na tsaro sakamakon yakin Iraki, shi Ehud Olmert ko rufa-rufa baya yi game da haka.

“Kifar da mulkin Saddam Hussein a Iraki tamkar gobarar titi ce a gare mu, saboda mu kam gaba ta kai mu. A saboda haka muke godiya ga Allah da ya bai wa George W. Bush wannan jumuri da karfin zuciya wajen tafiyar da wannan lamari.”

To sai dai kuma ba dukkan manazarta al’amuran tsaron Isra’ila ke marhabin da manufofin shugaba Bush na kasar Amurka ba, wanda a halin yanzu haka yake kaka-nika-yi da matsalar Irakin. Misali tsofon ministan harkokin wajen Isra’ilar Shlomo Ben-Ami na tattare da imanin cewar akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin rashin nasarar babbar daular ta duniya a kasar Iraki da yakin baya-bayan nan na kasar Lebanon. Kungiyoyin Hizballah da Hamas sun koyi darasi ne daga abubuwan dake faruwa a Iraki, wanda ke ba su kwarin guiwar cewar hare-hare na sare ka noke shi ne nagartaccen mataki na kalubalantar wata babbar daula kamar Amurka. Bugu da kari kuma tuni martabar kasar ta Amurka ta zube a idanun jama’a a yankin gabas ta tsakiya ta yadda ya zama wajibi akanta ta nemi hadin kai, ba ma kawai daga kasashen Rasha da China da na yammacin Turai ba, har ma da kasashen Siriya da Iran, saboda rikicin Iraki tuni ya zama rikici na shiyya kuma a saboda haka ya zama wajibi a nemi wata hanya bai daya domin warware shi.