1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani ya mamaye alakar mawakan Nijar da Faransa

September 15, 2023

Faransa ta ce ba ta da niyyar katse hulda ta bangarena al'adu da kasashen Nijar da Burkina Faso da Mali.

https://p.dw.com/p/4WOGz
Hoto: Arif Hudaverdi Yaman/AA/picture alliance

Ma'aikatar kula da al'adu ta kasar ce ta yi wannan karin haske bayan sanar da dakatar da wasu yarjejeniyoyi da ke tsakaninta da mawaka da ke wadannan kasashe na Afirka da juyin mulkin kasashensu ya lalata alakarsu a fannin diflomasiyya.

Ministar kula da harkokin al'adun Faransa Rima Abdul-Malak ta sanar a wannan Juma'a cewa akwai wasu yarjeniyoyi masu yawa da haramcin farko ba zai shafe su ba, amma ta ce akwai bukatar wasu daga cikin mawakan su nemi takardar izinin shiga Faransa sabanin yadda suke yi a baya a karkashin tsohuwar yarjejeniyar da suke da ita da Faransa kafin juyin mulkin da aka yi a kasashensu.

Sai dai kuma tuni kungiyar SYNDEAC wadda ta kunshi mawaka da sauran masu ayyuka na al'adu a Faransa ta sanar da nuna bacin ranta a kan wannan mataki da Faransan ta dauka a kan abokan aikinsu da ke Afirka.