Al´adar kaɗa goge tsakanin Abzinawa | Zamantakewa | DW | 09.10.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Al´adar kaɗa goge tsakanin Abzinawa

Hira da Hajiya Ajo mashahuriyar mai kaɗa gogen al´umar Abzinawa a Janhuriyar Nijer.

default

Taswirar Janhuriyar Niger

A yau shirin na mu zai yada zango ne a jihar Agades ta Janhuriyar Nijer, inda wakilinmu Mahaman Kanta ya samu yin hira da wata dattijuwa wadda ta yi fice kan kaɗa gogen al´ummar Abzinawa da ake kira Hajiya Ajo. Bisa al´adar al´ummar Abzinawa mata ne ke kaɗa goge kuma suna kaɗa shi ba a matsayin moraƙa ba, a´a suna wasa jarumai ne ko su bayyana wani abu na tarihi ko kuma soyayya. Ita dai wannan jatumar dai ta manyanta amma babu magajiya saboda haka take baƙin ciki tare da nuna damuwa ganin ´yan matan yanzu sun yi watsi da wannan al´adar.

To da fatan za a samu waɗanda za su gaje wannan dattijuwa wajen kaɗa goge don ka da da zara ta kau wannan al´adar kuma ta kau.

Sauti da bidiyo akan labarin

 • Kwanan wata 09.10.2008
 • Mawallafi Awal, Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/FWe3
 • Kwanan wata 09.10.2008
 • Mawallafi Awal, Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/FWe3