1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al zawahiri ya kushe matakin Mr Bush game da Iraqi

Mataimakin shugaban kungiyyar Alqa´eda wato, Aiman Al Zawahiri ya kushe matakin da Shugaba Bush ya dauka na karin yawan sojoji a Iraqi.

A cikin wani sako daya aike izuwa yanar giza gizan sadarwa na Internet, Al Zawahiri ya kalubalanci shugaban na Amurka daya aike da duk dakarun sojin na Amurka izuwa Iraqi.

A cewar mataimakin shugaban kungiyyar na Alqa´eda, aikewa da yawan soji izuwa iraqi ba itace mafita ba.

Mafita a cewar sa itace ficewar dakarun sojin kawance daga cikin kasar ta Iraqi.

A dai farko farkon watan nan da muke ciki ne, shugaban na Amurka ya bayar da sanarwar karin soji dubu 20 izuwa Iraqi, don taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar baki daya.