Al-Zarqawi ya nuna fuskar sa a cikin wani faifayen bidiyo | Labarai | DW | 26.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Zarqawi ya nuna fuskar sa a cikin wani faifayen bidiyo

A karon farko mutumin nan da ayyana kansa a matsayin shugaban kungiyar al-Qaida a Iraqi ya bayyana a cikin wani faifayen bidiyo da aka saka a shafin intanat na wata kungiyar masu kishin Islama. Jami´an leken asirin Amirka sun ce Abu Musab al-Zarqawi ke cikin wannan faifayen bidiyon wanda aka dauka a ranar 21 ga watannan na afrilu. Kawo yanzu dai shugaban na ´yan al-Qaida a Iraqi ya na tura sakonninsa ne ta recodar daukar magana. Yanzu haka dai jami´an Amirka na kokarin tabbatar da sahihancin bidiyo din wanda a ciki Zarqawi ya ce Amirka zata kwashi kashinta a hannu a Iraqi. Amirka ta ware ladan dala miliyan 25 ga wanda ya nuna mata inda Al-Zarqawi yake.