Al-Shabaab ta kai hari a Somaliya | Labarai | DW | 25.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Shabaab ta kai hari a Somaliya

Kungiyar Al-Shabaab ta kai wasu tagwayen hare-hare a wani otel da ke Mogadishu babban birnin kasar Somaliya tare da hallaka mutane 28 kana wasu 43 kuma suka jikkata.

Raahotanni dai sun nunar cewa mayakan na al-shabaab sun yi amfani da wata mota ne da ke makare da bama-bama wajen fasa kofar shiga otel din mai suna Otel Daya da ke kusa da majalisar dokokin kasar wanda kuma 'yan siyasa ke yawan zuwa can. Daga cikin wadanda suka jikkatan kuwa har da wasu 'yan jarida guda hudu wadanda suka je domin daukar rahotonni.