Al-Qaida ta kai mumunan hari a ma′aikatar tsaro a Siriya | Labarai | DW | 25.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Qaida ta kai mumunan hari a ma'aikatar tsaro a Siriya

Wani harin kunar bakin wake da aka kai a cibiyar tsaro ta soja da ke birnin Homs a Siriya, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42 daga cikinsu har da shugaban ma'aikatar tsaron Hassan Daaboul.

Kungiyar kare hakin bil-Adama ta kasar ta Siriya ce dai ta bada adadi, yayin da gwamnan jihar ta Homs Talal Barazi, ya ba da adadin mutane 30 da suka mutu, da kuma wasu 24 da suka samu raunuka. Wannan hari dai ya kasance mafi muni da aka kai a birnin na Homs a cewar  Rami Abdel Rahmane shugaban kungiyar kare hakin bil-Adama ta kasar ta Siriya.Tuni dai tsofuwar kungiyar Al-Qa'ida a kasar ta Siriya ta dauki alhakin kai harin, a daidai lokacin da ake kokarin tattaunawa tsakanin bangaran gwamnatin ta Siriya da 'yan adawa a birnin Jiniva. A hannu daya kuma adadin wadanda suka mutu a harin da Kungiyar IS ta kai a ranar Juma'a kusa da birnin Al-Bab ya kai na mutane 77 cikinsu fararan hulla 41.