Akwai barazanar ƙarancin abinci a kasashen Afrika dake fama da ambaliya | Labarai | DW | 19.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Akwai barazanar ƙarancin abinci a kasashen Afrika dake fama da ambaliya

Ma´aikatar ba da taimakon raya kasashe masu tasowa ta tarayyar Jamus ta ware kudi euro dubu 500 a matsayin taimakon gaggawa ga kasashen Afirka da ke fama da masifar ambaliyar ruwa. Ita kuma kungiyar ba da taimakon abinci ta Jamus ta sanar da ba da taimakon euro dubu 100 ga ´yan gudun hijira daga ambaliyar ruwan arewacin kasar Uganda. Kiyasin MDD ya yi nuni da cewa sama da mutane miliyan daya da rabi na kasashen Afirka kudu da Sahara, mummunar ambaliyar ruwan ta shafa. A kuma halin da ake ciki MDD ta yi kashedi game da fuskantar karancin abinci sakamakon ambaliyar ruwa. Ta ce ana bukatar taimakon gaggawa na dala miliyan 65.