Akwai alamun samun nasara a tattaunawar Hamas da Fatah a Saudiya | Labarai | DW | 08.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Akwai alamun samun nasara a tattaunawar Hamas da Fatah a Saudiya

Rahotanni sunce akwai alamun cewa tattaunawar birnin Makka tsakanin kungiyoyin Hamas da Fatah ta fara samun nasara.

Wani na hannun daman shugaba Mahmud Abbas na kungiyar Fatah yace ya kamata kwararru masu zaman kansu su shugabanci wasu maaikatu na gwamnatin hadin gwiwar ta Palasdinawa.

Maaikatun kuwa sun hada da maaikatar kudi,da ta harkokin cikin gida da kuma waje.

Dukkanin bangarorin biyu dai sunyi alkawarin ci gaba da tattaunawa har sai an cimma yarjejeniya data dace.

Shugaban kungiyar Hamas dake gudun hijira Khaled Mashaal ya bukaci magoya bayan kungiyoyin Hamas da Fatah dasu mutunta yarjejeniyar data fara aiki a ranar lahadi.