Akalla mutum 100 sun rasu a wani rikicin kabilanci a kasar Chadi | Labarai | DW | 07.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Akalla mutum 100 sun rasu a wani rikicin kabilanci a kasar Chadi

Gwamnatin kasar Chadi ta ce an kashe mutane fiye da 100 a wani tashin hankali da aka yi a makon jiya tsakanin Larabawa da wadanda ba larabawa ba na wannan kasa. Ministan kula da kananan hukumomi na Chadi Ahmat Mahamat Bashir ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewar an fara tahomugaman ne a karshen watan oktoba tsakanin Larabawa da ´yan kabilar Kibet a kudu maso gabashin kasar. Wani ma´aikacin wata kungiyar kare hakkin bil Adama ya tabbatar da aukuwar hargitsin.