Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu a hadarin dakin wasannin kankara a Jamus | Labarai | DW | 03.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu a hadarin dakin wasannin kankara a Jamus

Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu fiye da 20 suka jikkata,biyowa bayan rushewar rufin wani dakin wasannin kankara a garin Bad Reichenhall,a kudancin Jamus.

Yan sanda sunce har yanzu basu san ko mutane nawa ne suke binne karkashin rufin ba,wanda ya rusa saboda nauyin dusar kankara data sauka a yankin.

Wakilin Dw Karl Frierich Broderix,yace,maaikatan agaji na ci gaba da kokarin nemo wadanda har yanzu suke da ransu cikin hadarin.

Shi kuma magajin garin,ya karyata zargin cewa an san cewa wannan rufi zai iya rusawa karkashin nauyin kankara,inda yace an rigaya an auna yawan dusar kankarar dake kann rufin ssaoi kadan kafin abkuwar hadarin kuma sun gano cewa babu wani abin damuwa ciki.