Aikin rajistar masu zaɓe a Nijeriya | Labarai | DW | 07.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aikin rajistar masu zaɓe a Nijeriya

Hukumar zaɓen Nijeriya ta bayyana cewar nan da kwanaki 35 masu zuwa ne za ta karɓi kayayyakin gudanar da aikin rajistar masu zaɓe

default

Shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya

Hukumar zaɓe a Nijeriya mai zaman kanta wato INEC ta ce ta sanya hannu akan yarjejeniya tare da kamfanonin da za su samar mata da kayayyakin da za'a yi amfani da su wajen aikin rajistar masu zaɓe a ƙasar. Wata sanarwar da hukumar zaɓen ta fitar a wannan Lahadin, ta ce a ƙarƙashin yarjejeniyar, za ta sami ƙananan na'urorin Computer tafi da gidan ka na Laptop guda 132,000, da kuma kayayyakin yin aikin rajistar, wanda hukumar ta ce a watan Janairu ne za ta yi. Hakanan sanarwar ta ƙara da cewar nan da kwanaki 35 ne hukumar za ta karɓi waɗannan kayayyakin.

Nijeriya, wadda ƙiyasi ya nuna cewar tana da yawan al'umma miliyan 150, ta gudanar da zaɓukan da aka yi sukar su a lokuta daban daban tun bayan sake komawar ta bisa turbar dimoƙraɗiyya kimanin shekaru 10 da suka gabata. Jami'ai sun ƙiyasta cewar ƙasar na da mutane miliyan 70 da suka cancanci ka'ɗa ƙuri'un su a zaɓen shugaban ƙasar da zai gudana baɗi idan Allah ya kaimu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal