Aikin nukiliyar Iran ya kusa kai ƙololuwar sa | Labarai | DW | 25.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aikin nukiliyar Iran ya kusa kai ƙololuwar sa

Shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nejad ya ce aikace aikace nukiliyar kasar ya kusa kai kololuwarsa. A lokacin da yake jawabi a gaban wani taron gangami a garin Isfahan dake tsakiyar kasar, shugaba Ahmedi Nejad ya ce Teheran ba zata taba saduda a shirin ta na nukiliya sakamakon matsim lambar kasashe yamma ba. Hakan dai ya biyo bayan kalaman da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta MDD Mohammed el-Baradei yayi ne cewa nan da shekaru 3 zuwa 5 masu zuwa Iran zata iya kera makaman nukiliya. A jiya alhamis shugaban Amirka GWB ya ce zai yi aiki tare da kawayensa na Turai da Rasha da kuma China don tsananta takunkumai akan Iran saboda nuna taurin kai ga bukatun MDD na ta dakatar da sarrafa sinadarin uranium. Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce yana goyon bayan warware wannan takadama ta hanyoyin diplomasiya.