1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin MINURSO a Yammacin Sahara na cikin tsaka mai wuya

Hilke Fischer/ YBApril 28, 2016

Shekaru 25 ke nan Majalisar Dinkin Duniya ke da tawaga a Yammacin Sahara. Ana maganar tsawaita aikinta, amma dangankata tsakanin Majalisar da Maroko ta yi tsami abin da ke saka ayar tambaya kan aikin tawagar.

https://p.dw.com/p/1Ieox
MINUROSO
Hoto: AFP/Getty Images

A yayin da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya a Yammacin Sahara ke cika shekaru 25 a wannan Juma'a, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar a zamansa na ranar Alhamis din nan ya sake nazari na yiwuwar kara wa'adi na ci gaba da aikin wanzar da zaman lafiya a yankin bayan da ake samun rabuwar kawuna kan wannan aiki na tawagar MINURSO.

Tuni dai Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar sake fadawa wani yanayi na sabon yaki muddin aka janye ayyukan na MINURSO. Kungiyoyi na 'yan ta'adda za su yi amfani da damar raunin da aikin wanzar da zaman lafiyar na Majalisar Dinkin Duniya ke da shi a yanzu, bayan da kasar Maroko ta sallami wasu ma'aikatan majalisar da ke aiki a wannan yanki.

Ba a tabuka abin kirki a Yammacin Sahara ba

Yammacin na Sahara dai na karkashin mulkin mallakar kasar Spain ne, sai dai Maroko ta samu 'yancin iko da shi a shekaru gommai na 1970.

Algerien UN Generalsekretär Ban Ki Moon in Tindouf
Ban Ki Moon lokacin ziyararsa a TindoufHoto: picture-alliance/dpa/adel Sehrei/Wostok Press

A lokacin ziyararsa a watan Maris na wannan shekara ta 2016 Mista Ban ya bayyana cewa babu ci gaba da aka samu kan wannan aiki da ya faro tun a shekarar 1991 a yankin na Sahara da ke da fadin kasa kamar Italiya wanda ke karkashin "Iko na kasar Maroko" a cewar Mista Ban. Abin da masaurantar wannan kasa suka nuna rashin jin dadinsu da kalaman na Sakatare-Janar din. Hakan dai ya sanya mahukuntan kasar suka sallami ma'aikatan na MINURSO har guda 80 tare da barazanar tsaida tallafinsu a ayyukan dakarun majalisar.

Christos Tsatsoulis tsohon jami'i ne da ke sa idanu kan wannan aiki na MINURSO a bangaren soji ya bayyana cewa aikin tare da kasar ta Maroko abu ne mai muhimmanci.

"Kamar yadda na lura tallafin da kasar ta Moroko ke ba wa ayyukan na Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Maroko ko a Yammacin Sahara abu ne wanda yake da kyau. Idan har kasar Maroko za ta janye irin tallafin da take bayarwa a aikin na MINURSO to ba na jin aikin zai cigaba da dorewa."

Kusan mutanen kasar ta Maroko miliyan uku ne suka fito birnin Rabat tare da yin adawa da shirin masarautar kasar kan abin da suka kira yin ba daidai ba ga ma'aikatan na Majalisar Dinkin Duniya.

Parade zum 35. Jahrestag der Gründung der Polisario in Westsahara
Faretin cika shekaru 35 da kafa kungiyar Polisario a Yammacin SaharaHoto: picture-alliance/dpa/M. Messara

Masu fafutika daga bangaren Saharawi Arab Democratic Party a shekarar 1976 sun fantsama yaki da dakarun sojan kasar Maroko har sai da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya a shekara ta 1991.

Tawagar MINURSO ta yi rawar gani

Sabanin maganar da babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ke cewa, Helmut Reifeld jami'i a ofishin gidauniyar Konrad-Adenauer ta Jamus a Moroko ya ce ba za a ce aikin na MINURSO bai tabuka komai ba.

"Har yanzu aikin na bisa turba tun da ya samu dama ta shawo kan matsalar da ta gagara karkashin dokar kasa da kasa wacce har yanzu ke bukatar samun mafita. A cigaba da kokari don samun sauyi na zaman lafiya."

Membobi dai na kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya na ganin babu yadda za a yi wannan tafiya ba tare da kasar ta Maroko ba, kamar dai yadda a nan ma Reifeld ke cewa.

"Tun bayan ballewar rikicin 'yan gudun hijira kasashen Turai na cigaba da sanya idanu kan kasar ta Maroko. Ba tare da wani bata lokaci ba ne ta amince da mayar da 'yan gudun hijirarta su koma gida."

Iyakokin na Yammacin Sahara wato gabar tekun Atilantika da yankinta ba a fitar da su ba karkashin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Maroko da kungiyar Tarayyar Turai, sai dai kasar ta shigar da yankin cikin harkokinta na tattalin arziki inda take ribatar albarkatu na karkashin kasa da suka hadar da na mai da kamun kifi da dai sauransu, abin da ya saba wa dokar kasa da kasa.