1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin kiyaye zaman lafiya a Dafur

June 7, 2006
https://p.dw.com/p/Buv1

Kwamitin tsaro na MDD tare da ƙungiyar gamaiyar Afrika sun cimma yarjejeniya a game da tura dakarun kiyaye zaman lafiya na ƙasa da ƙasa domin maye gurbin sojin ƙungiyar Afrika a lardin Dafur ba tare da jinkiri ba. Bayan tattaunawar da suka gudanar a ranar larabar nan a birnin Addis Ababa, ɓangarorin biyu sun baiyana cewa wajibi ne musayar sojojin ya sami sahalewar gwamnatin Sudan wadda har ya zuwa wannan lokaci bata yi amanna da ƙudirin ba. ƙungiyar gamaiyar Afrikan na da dakarun soji 7,000 waɗanda ke aikin kiyaye zaman lafiya a Dafur. A watan da ya gabata Sudan ta sanya hannu a kann yarjejeniyar sulhu da babbar kungiyar yan tawaye ta Dafur, to amma ragowar kungiyoyi biyu na yan tawayen sun ki amincewa da yarjejeniyar. Dubban jamaá sun rasa rayukan su a Dafur tun bayan da rikicin ya ɓarke a shekarar 2003 yayin da kuma mutane fiye da miliyan biyu da rabi suke gudun hijira.