1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin Hajjin bana ya kai ƙololuwarsa

November 15, 2010

A yau ake hawan dutsen Arafat a daidai lokacin da aikin Hajjin bana ya kai ƙololuwarsa

https://p.dw.com/p/Q8ZM
Musulmi akan dutsen Arafat yayin aikin Hajji. Da yawa daga cikinsu sun kwana a filin ArafatHoto: AP

Musulmi kimanin miliyan uku sun hallara a filin Arafat a yau Litinin domin gudanar da ɗaya daga cikin muhimman ayyukan ibada na Hajji. Hawa dutsen Arafat dai na zama ƙololuwar aikin Hajji. Ma'aikatar cikin gidan Saudiya ta ce a bana Musulimi kimanin miliyan 1.7 daga ƙasashen duniya kimanin 181 suka shiga daular ta ƙasa da ta ruwa da kuma ta sama domin gudanar da wannan ibada dake zama ɗaya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci guda biyar. An dai tsaurara matakan tsaro ga aikin na hawan Arafat ɗin a yau, musamman a birnin Minna dake gabas da birnin Makkah, biyowa bayan gobara da ta tashi wadda ta lalata tantuna 30 amma ba ta jiwa mutum ko da guda ɗaya rauni ba. Tudun Arafat da ake kuma kiransa Tudun Rahma, a nan ne Annabi Mohammad (tsrira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yayi huɗubarsa ta ban-kwana ga Musulmin da suka yi aikin Hajji kimanin shekaru 1400 da suka wuce. Da rana ta faɗi da yawa daga cikin Mahajjatan a ƙafa ko keken guragu ko a bas za su sauka daga tsaunin Arafat zuwa Muzdalifa. A bana dai an buɗe wani layin dogo na zamani da ƙasar China ta gina akan kuɗi dala miliyan dubu biyu, da ya haɗa Makkah, Minna da kuma Muzdalifa dake kan hanyar zuwa Arafat, ya sauƙaƙa wannan tafiya. Hukumomin Saudiya sun ce an rabawa Mahajjata lita fiye da miliyan 15 na ruwan Zamzam.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas