Aikin hajjin bana na tafiya lamun lafiya a kasa mai tsarki | Labarai | DW | 10.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aikin hajjin bana na tafiya lamun lafiya a kasa mai tsarki

Sama da musulmi miliyan biyu da ke aikin hajjin bana sun fara jifar shaidan a yau talata, a daidai lokacin da sauran al´umar musulmi a duniya baki daya ke bukin babbar Sallah. Da sanyin safiyau din nan wasu mahajjata suka isa wurin jifar shaidan kafin a samu cunkoso jama´a a wurin jifar shaidan. A cikin jawabinsa na bukin babbar Sallah Sarki Abdullah ya roki Allah SWT da ya bari wannan Idi ta zama ta zaman lafiya da kwanciyar hankali ga musulmi da duniya baki daya tare da hada kan musulmi cikin yarda da amincin Ubangiji. Shi kuwa a cikin hudubarsa ta Idi limamin masallacin Makkah Sheikh Abdulrahma al-Sudeis kira yayi ga musulmi da su tuna da ´yan´uwansu a Falasdinu da kuma Iraqi, wadanda ke cikin akuba tun bayan mamayar kasar da Amirka ta yi a cikin shekara ta 2003. A bana dai kasar Saudiyya ta girke jami´an tsaro kimanin dubu 60 don agazawa miliyoyin musulmi tare da dakile duk wani hari da masu kishin islama kai iya kaiwa a lokacin aikin hajjin.