Aikin Hajjin bana a Saudiya | Labarai | DW | 16.12.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aikin Hajjin bana a Saudiya

An kammala dukkan wasu shirye-shirye na tabbatar da doka da kuma oda, a lokacin aikin hajjin bana. Ministan cikin gida na Saudiya, Yarima Nayef bin Abdulaziz, ya ce an ɗauki matakan ne don kare lafiyar maniyya, a lokacin gudanar da aikin hajjin. Mahajjata sama da miliyan ɗaya da dubu ɗari shida ne ya zuwa yanzu su ka isa ƙasa mai tsarki, don gudanar da aikin hajjin bana.Ana sa ran mutane sama da miliyan biyu ne za su gudanar da aikin hajjin na bana a wannan shekara. A ranar talata ake sa ran hawa dutsen Arfa, dake ɗaya daga cikin muhimman ayyukan aikin hajji. Washe gari kuma laraba a cewar rahotanni a gudanar da Eid babbar Sallah.

 • Kwanan wata 16.12.2007
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/CcEk
 • Kwanan wata 16.12.2007
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/CcEk