1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Aikin dakarun Afrika a Somalia

Dakarun kungiyar Afirka (AU) zasu karbe karfin fada-aji a birnin Mogadishu

default

Wani Jami'in sojin AU ke sintiri a titin birnin Mogadishu

Cikin jawabin da ya yiwa manema labarai, jakadan kungiyar tarayyar Afrika (AU) a Somalia, Wafula Wamunyinyi, yace sannu a hankali dakarun gamayyar sojin wanzar da zaman lafiya na AMISON da suka fito daga kasashen Uganda da Burundi,  su kimanin 7,200 na karbe wurare da dama wadanda ke karkashin kulawar yan tarzoma, kana kuma suna kara tura su wajen birnin.

Bugu da kari kuma yace, " yanzu haka dakarun mu sun kwace kimanin kashi 40 cikin dari na yankunan, inda muke sa ran nan zuwa karshen watan da muke ciki, fiye da rabin yankunan da yan tarzomar suka mallaka zai dawo karkashin kulawar mu. Haka nan kuma Mr. Wamunyinyi, ya bada tabbacin cewa, mutanen dake zaune a yankunan da dakarun na AMISON suka kwato na samun damar gudanar da ayyukan su na yau da kullum cikin kwanciyar hankali, duk kuwa da cewar ba za a iya dauke tsammanin yan hare-hare daga yan tarzoma ba.

A tattaunawar da yayi da wakiliyar DW, jim kadan bayan ganawar sa da wakilan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Shugaba Yoweri Museveni, yace kasar sa na bukatar tura karin sojoji zuwa Somalia.

Yoweri Museveni, Präsident von Uganda

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ke amsa tambayoyin yan jarida.

" Uganda a shirye take ta tura karin sojoji zuwa Somalia, idan damar hakan ta samu. Yanzu haka dai bamu da kudi, to amma matukar al'umomin kasa da kasa zasu tallafa, mukam muna da kwararrun dakaru kuma a shirye suke su fafata, rashin kudi shi ne matsala"

Kimanin kungiyoyin yan tarzoma biyu ne dai suka share shekaru uku suna kai hare-hare da nufin hambarar da gwamnatin rikon kwaryar ta Somalia dake samun goyon bayan kasashen yamma, wadda masana ke cewa na fama da matsalolin cin hanci da karbar rashawa.

A ta bakin jami'ar kula da harkokin ketaren kungiyar tarayyar turai ta (EU) Catherine Ashton, kungiyar ta EU wadda ita ce kangaba wajen bawa kasar ta Somalia taimako domin cigaba gami da sake gina kasar, tace zata cigaba da bada taimakon ta har ma ga yankin Puntaland dake kokarin cin gashin kansa daga kasar ta Somalia.

Cikin makon nan ne dakarun wanzar da zaman lafiya na AU da hadin gwiwar sojin gwamnati suka shafe kwanaki 6 suna fafatawa da yan tawaye babu kakkautawa. Wani jami'in kula da motar daukar marasa lafiya a yankin mai suna Ali Muse, yace kimanin sama da mutane 40 suka rasu, kana wasu daruruwa suka gujewa muhallan su, sakamakon wannan taho mu gama.Dangane da bukatar karin sojoji daga Uganda, domin kawar da aukuwar irin wannan lamari a gaba, kakakin sojin kasar, Felix Kulayijye, ya kara da cewa " hakan zai yiwu ne matukar al'umomin kasa da kasa da MDD zasu bada goyon baya gami da tallafin kudade kan al'amuran kasar Somalia, ko a samu saukin lamura. Ba wai muna neman wani abu mai yawa ba"

Tuni dai kungiyar al'shabab dake da karfin fada aji a yankin tsakiya dama kudancin Swathes, ta kulle kan iyakar Somalia da Kenya, ta hanyar tura dakarun ta dauke da makamai, inda suke dakatar da duk wata mota dake kokarin shiga ko kuma fita daga kasar, lamarin da ya  jawo gurgunta harkokin sufuri a yankin.

Mawallafi : Tukur Garba Arab

Edita : Abdullahi Tanko Bala