Aikin ceto a kasar Turkiya | Labarai | DW | 26.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aikin ceto a kasar Turkiya

Maáikatan agaji sun kai dauki domin ceto mutane wadanda ginin ya rubta da su a birnin Istanbul na kasar Turkiya. Baá sami tabbaci a game musabbabin faduwar ginin mai hawa takwas ba. Sai dai a waje guda gwamnan birnin na Istanbul Muámmar Guler yace jamaá da dama mazauna rukunin gidajen sun kaurace saá guda kafin faduwar ginin, bayan da suka ji rugugi na alamun zai fadi. Rahotanni sun ce ginin ya dan yi lahani bayan girgizar kasa ta shekarar 1999 a wannan yankin. An dai dora laifin rashin ingancin gine gine a kasar Turkiya da haddasa hasarar rayukan dubban jamaá musamman a yayin da girgizar kasa ta auku.