1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin bada agaji ga mutanen da suka tagaiyara a Kashimir

October 18, 2005
https://p.dw.com/p/BvOy

Dubban jamaár da suka tagaiyara a sakamakon girgizar kasa a yankin Kashimir na kasar Pakistan na cigaba da rayuwa cikin mawuyacin hali na rashin matsuguni da harkokin lafiya yayin da a hannu guda hukumomi ke kashedin cewa barkewar cutattuka da kuma tsananin sanyi ka iya jawo hasarar wasu rayukan. Sojojin Pakistan da maáikatan agaji na farar hula tare da hukumomin bada agaji na kasa da kasa na cigaba da kai gudunmawar abinci da likitoci zuwa ga yankunan da guirgizar kasar ta yi taádi. Datsewar hanyoyi a sakamakon girgizar kasar ya haifar da tsaiko wajen kaiwa ga wasu yankunan dake bukatar taimako. A halin da ake ciki jiragen sama masu saukar ungulu sun fara jigilar kai kayan abinci tsaiko na dan lokaci saboda tsananin ruwan sama kamar da bakin kwarya.