1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin agaji a Pakistan ya kama hanyar tagayyara

October 27, 2005
https://p.dw.com/p/BvNj

Wasu daga cikin kasashen duniya sunyi alkawarin taimakawa da masu gidan rana har rabin biliyan daya dalar Amurka ga kasar Pakistan.

Wannan tallafin dai yazo ne bayan da Sakataren Mdd Kofi Anan ya kara daukaka kira ga kasashe masu hannu da shuni nasu kara tallafawa kasar ta Pakistan don amfani da kudin wajen gudanar da aiyukan bada agaji ga wadanda bala´in girgizar kasar nan ya rutsa dasu.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa wannan kira da Kofi Anan din yayi nada nasaba ne da rashin kudi da hukumomi na Mdd masu bada aikin ceto suka fada, wanda hakan ke neman kawo cikas game da aiyukan da suke gudanarwa a kasar.

Wannan dai girgizar kasa data faru a ranar takwas ga watan nan da muke ciki a yanzu haka an kiyasta cewa tayi ajalin mutane dubu hamsin da biyar, wasu kuma dubu 74 sun jikkata, kana a daya hannun mutane miliyan uku sun rasa gidajen kwanan su.