AIDS a Jamus | Zamantakewa | DW | 28.11.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

AIDS a Jamus

Alkaluman kwanakin baya bayan nan na nuna cewa ana samun habakar yawan masu kamuwa da cutar AIDS a nan Jamus. A cikin farkon watanni 6 na wannan shekarar an sami karin kashi 20 cikin dari fiye da adanin wannan lokacin a shekarar bara.

Tallata kayan riga kafi ga AIDS a Jamus.

Tallata kayan riga kafi ga AIDS a Jamus.

Tun fiye da shekaru 5 da suka wuce ke nan ake ta kara samun yawan masu kamuwa da cutar AIDS a nan Jamus. A cikin farkon watanni 6 na wannan shekarar, an sami karin kashi 20 cikin dari na mutanen da suka kamu da cutar, idan aka kwatanta alkaluman bana da na shekarar da ta wuce. daya daga cikin dalilan da jami’an kafofin kiwon lafiya suka ce suna janyo hakan kuwa shi ne, an rage takalo batun yaduwar cutar a bainar jama’a da kuma kafofin yada labarai. Sabili da haka, mutane da dama ba sa la’akari da barazanar da take dauke da ita. Kamar yadda Sven Christian Finke, shugaban kungiyar sa kan nan ta AIDS-Hilfe ya bayyanar:-

„A bangare daya, kamfanonin sarrafa magunguna dai na tallata magungunansu ne da masu kame da cutar za su dinga sha, amma ba sa ambatar daukan matakan riga kafi, da kuma sakamakon da rashin yin hakan zai haifar. A nawa ganin dai, irin wannan halin na samun angizo a bainar jama’a, ta yadda mutane da yawa ba sa daukar barazanar kamuwarsu da cutar kuma da muhimmanci.“

A halin yanzu dai, akwai ingantattun hanyoyin kula da masu kame da cutar a nan Jamus fiye da da. Amma a bangare daya kuma, sai ka ga kamar mutane ba su damu ba ma da daukan matakan kare kansu, inji Elisabeth Pott, shugaban cibiyar fadakad da jama’a kan batutuwan da suka shafi kiwon lafiya ta nan Jamus. Ta kara da cewa:-

„Bai kamata dai a manta da cewa, inganta hanyoyin kula da masu kame cutar, ba magance ta ba ne. Ko da yake marasa lafiyan na samun sauki, amma duk da haka, ba sa iya tafiyad da halin rayuwarsu kamar a lokacin da ba su kamu da cutar ba, saboda magungunan ma na janyo musu illoli da dama, har ma ya sa su iya kamuwa da wasu cututtukan daban kuma.“

Cutar AIDS dai har ila yau ba a sami maganin warkad da ita ba tukuna. Sabili da haka ne kafofin kiwon lafiya ke gargadi ga jama’a, maza da mata, da su yi taka tsantsan wajen saduwa ba tare da sanin juna, ko kuma daukan matakan kare kansu ba. Akwai dai jami’an kiwon lafiya da yawa da aka horar, wadanda ke zuwa gun taruwar `yan luwadu da masu shan kwayoyi don su fadakad da su kan illolin wannan cutar da kuma barazanar da z ata iya janyo wa rayukansu. Suna kuma ba da shhawarwari a kan shafin yanar gizo ta Internet.

kwararrun masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa, Jamusawa sun fi `yan kasashen da dama samun bayanai kan yaduwar wannan cutar ta AIDS. Amma a ko yaushe, ya kamata a yi ta ci gaba da fadakad da matasa.

Wani binciken da aka gudanar kuma na nuna cewa, duk da yunkurin fadakad da jama’a da ake yi a nan Jamus, baki mazauna kasar ba su da cikakkiyar masaniya game da yaduwar cutar. Kazalika kuma, da yawa daga cikinsu ba sa tuntubar kafofin fadakad da jama’a da aka bude a duk fadin kasar. kungiyar AIDS-Hilfe dai na ganin cewa, rashin iya yaren Jamusancin ma na daya daga cikin dalilan da ke hana bakin zuwa neman taimako a wadannan kafofin. Sabili da haka ne dai take yunkurin daukan ma’aikata baki, wadanda za ta horar, don su iya yi wa `yan uwansu baki masu neman taimako bayanai a cikin harsunansu na asali.

 • Kwanan wata 28.11.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUD
 • Kwanan wata 28.11.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUD