Ahmedinejad zai halarci taron zaman lafiyar Iraqi | Labarai | DW | 29.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ahmedinejad zai halarci taron zaman lafiyar Iraqi

Ministan harkokin wajen Iraqi Hoshiyar Zebari ya bada tabbacin cewa shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmedinejad zai halarci taron kasa da kasa da zaá gudanar a Masar da nufin samo hanyoyi sasanta alúmomin Iraqi da kuma kawo karshen rikicin dake gudana a kasar. Zebari yace akwai kyakyawan fata Iran da Amurka za su zauna su fuskanci juna ta fuskar diplomasiya a yayin taron. Yana mai cewa hakan zai kasance babban matakin cigaba na wanzar da zaman lafiya a Iraqi. Rahotanni daga birnin Tehran kuma na cewa tuni babban jakadan Iran Ali Larijani ya tashi zuwa birnin Bagadaza domin tattaunawa da mahukuntan Iraqin a game da taron.