Ahmedinajad yace kasarsa bata da burin mallakar makaman nukiliya | Labarai | DW | 24.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ahmedinajad yace kasarsa bata da burin mallakar makaman nukiliya

Shugaban kasar Iran Mahmud Ahmedinajad yace kasar Iran bata bukatar makaman nukiliya haka zalika bata shirin fafata yaki da kasar Amurka.Kafin tashinsa zuwa babban taron MDD a birnin New York,Ahmedinajad ya baiyanawa gidan TV CBS na Amurka da kakkausar murya cewa Iran bata da niyar mallakar makamin nukiliya.Batun baiwa shugaban na Iran damar yin jawabi a jamiar Columbia ya janyo adawa daga wasu dake cewa bai kamata jamiar ta bashi damar jawabi gaban dalibanta ba,bayan ya karyata kisan gilla na yahudawa,bayan kuma Amurka tana zarginsa da goyon bayan taadanci.