Ahmed Shafiq na Masar zai tsaya takara
April 26, 2012Hukumar zaɓen Masar ta amince da takarar firaministan da ya yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin hambararren shugaba Hosni Mubarak a zaɓen shugaban ƙasar da za'a gudanar a watan Mayu idan Allah ya kai mu, abun da ya juya shawarar da ta fara yankewa akan dan takarar. Ahmed Shafiq yana daga cikin jami'an gwamnatin da ke aiki lokacin da guguwar neman sauyi ta kaɗa a ƙasar daga farkon shekarar 2011, ta kuma kai ga hamɓarar da Mubarak daga karagar mulkin Masar.
Wannan shawarar dai ta saɓa wa dokar da majalisar dokokin ƙasar ta kafa, wacce ta haramta wa duk wani wanda ya riƙa babban muƙami ƙarƙashin gwamnatin Mubarak takara a zaɓen bana. Kawo yanzu dai 'yan takara 10 ne hukumar zaɓen ta dakatar bisa dalilai daban-daban. Amma kuma ana sa ran a wannan alhamis zata kammala tantance 'yan takarar, ta kuma gabatar da wadanda ta amince da su.
Mawallafi: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe