Ahmadi Nedjad a Algeria | Labarai | DW | 07.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ahmadi Nedjad a Algeria

Shugaban ƙasar Iran Mahmud Ahmadinedjad, ya kai ziyara aiki a ƙasar Algeria, inda ya gana da takwaran sa Abdel Aziz Buteflika.

Magabatan 2, sun yi masanyar ra´ayoyi, a game da batutuwa daban-daban da su ka shafi mu´amila tsakanin Algers da Teheran ,da kuma halin da ake ciki a rikicin gabas ta tsakiya.

Buteflika, ya bada cikkaken goyan baya, ga ƙasar Iran a game da rikicin nuklea.

Ya bayyana yancin Iran na mallakar makamashin nuklea, matakin da Amurika da ƙasashen turai ke adawa da shi.

A lokacinda ya gabatar da nasa jawabi Mahmud Ahmadinedjad ya jaddada matsayin sa na babu gudu babu ja da baya,a game da wannan rikici.

Sannan kamar yada ya saba, ya bayyana kalamomin haramta ƙasar Isra´ila.