Agajin cimaka na duniya ga jamhuriyar Niger | Labarai | DW | 26.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Agajin cimaka na duniya ga jamhuriyar Niger

Hukumar Abinci ta duniya ta yi alƙawarin ninka agajin cimaka ga jamhuriyar Niger da al´umarta ke fama da ja´ibar yunwa.

default

Awon hatsi a Niger

Hukumar abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi alƙawarin ruɓanya tallafi cimaka da ta ke baiwa jamhuriyar Niger sakamakon yunwa da ta fara addabar wasu sassan ƙasar.. Hukumar ta nunar da cewa ƙasar ta Niger na daga cikin sahun ƙasashen yankin Sahel da ke matiƙar bukatan agajin abinci saboda daminin bara ba ta yi albarka a garesu ba. PAM ta yi kira ga ƙasashen duniya da suka ƙara ƙayama wajen taimaka na kasar ta Niger. Darektar hukumar wato Josette Sheeran ta ce suna kan girka wani tsarin da kan iya taimaka wa mutun dubu 860.

Hukumomin Niger sun ce mutane a ƙalla miliyion 3 da rabi ne ke buƙatar agaji na gawgawa. Sai dai wata ƙungiyar mai zaman kanta ta ƙasar ta nunar da cewa yuwar na iya shafar mutane milliyion 7 da rabi, wato kimani kashi 58 cikin ɗari na yawan al umar ƙasar.

Mwallafi: Mohmmed Auwal Balarabe

Edita: Halima Abbas