Agajin abinci a Nijar | Labarai | DW | 15.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Agajin abinci a Nijar

Gwamnati da ƙungiyoyin bada agaji, sun fara raba abinci a ƙauyukan Jamhuriyar Nijar

default

Auna hatsi a Nijar

A safiyar yau ɗin nan ne a Garin Alhaji dake a nisan kilomita 55 da birnin Tahoua na Jamhuriyar Nijar, aka ƙaddamar da bukin soma bayar da abinci kyauta ga waɗanda yunwa ta fi yiwa barazana. Kakakin gwamnatin mulkin sojan Nijar Kanal Abdulkarim Gukoye shi ne ya jagoranci ƙaddamar da soma rabon abincin, yana mai cewa: "Wannan dai gomnatin Nijar ce da haɗin gwiwar hukumar kula da abinci duniya ta World Food Program suka shirya wannan taimakon, inda za'a raba ton 21 na shinkafa da dawa ga mutane mabuƙata da yawansu ya kai kusan miliyan ɗaya da rabi a faɗin ƙasar ta Jamahuriyar Nijar."

A na shi ɓangare wakilin hukumar kula da abinci ta Majalissar Ɗinkin Duniya, Richard Verbeeck, ya yabama jan ƙoƙarin da ƙasashe kamar su Faransa, Italiya, Canada, Jamus da dai sauransu suka yi, na amsa kiran gwamnatin Jamhuriyar Nijar na kawo tallafin abinci: "Fatan mu shi ne har zuwa ƙarshen damana kar wannan iyalan su canza yanayin abincin su, sabo da yunwa, ba mu fatan su shiga cikin wani mawuyacin hali sabili da rashin abinci, kuma ba ma fatan su shiga cikin bashi sabili da rashin abinci, dan haka muna so ne mu kuɓutar da su ga faɗawa cikin bashi."

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammad Nasiru Awal