Agaji zuwa Indonesia | Labarai | DW | 28.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Agaji zuwa Indonesia

Opishin ministan harakokin wajen Indonesia, ya bayana ƙaruwar yawan mutanen da su ka rasa rayuka a sakamakon mummunar girgizar ƙasa, da ta rutsa da yankin Java ranar jiya asabar.

Sabuwar ƙiddidigar da a ka gudanar ta bayana cewa, a ƙalla mutane 4.285 su ka riga mu gidan gaskiya.

A halin da ake ciki,Ƙasashe da ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa, na ci gaba da kai taimako ga yankin.

Banda asara rayuka,wannan sabuwar masifa, da ta wakana a tsibirin Java, ta raunana mutane fiye da 10. 000 , sannan a kalla mutane dubu 20 sunrasa matsugunai, inji mataimakin shugaban ƙasa Yusuf kalla.

Ya ce a halin da ake ciki, jami´an kulla da agaji, na fuskantar karancin kayan aiki, duk da taimakon gaggawa da ƙasashen dunia ke ci gaba da kaiwa.

Asibitocin ƙasar sun cika sun batse, a yayin,da har yanzu, a ke zaƙullo mutane daga cikin ɓaraguzai.