Agaji ga mutanen da bala'i ya shafa a Indonisiya
October 28, 2010Adadin mutanen da girgizar ƙasa ta karƙashin teku ko kuma tsunami da kuma aman dutse a ƙasar Indonisia ya yi sanadiyyar mutuwar sau ya kai kimanin mutane 343, a yayin da wasu 400 kuma - har yanzu ba'a san wurin da suke ba, kana wasu dubbannin kuma suka rasa matsugunan su. Fiye da ƙauyuka 13 ne ruwa ya shafe a tsibirin Mentawi dake yammacin Sumatra na ƙasar ta Indonisia bayan wani girgizar ƙasa ta ƙarƙashin ruwan da ta afku a ranar Litinin da ta gabata.
A yanzu dai Jirgin sama na farkon da ke ɗauke da kayayyakin agajin da suka haɗa da tantuna da magunguna da kuma sauran kayayyakin amfanin yau da kullum ya sauka a tsibirin, amma ma'aikatan ceto sun yi amannar cewar har yanzu ba su kai ga wuraren da matsalar ta fi muni ba. A halin da ake ciki kuma can a yankin kudancin ƙasar, abubuwa sun ɗan lafa bayan aman wutar da dutsen Merapi dake tsibirin Java ya yi a ranar Talata, wanda ya janyo turnuƙewar sararin samaniya da toƙa kana da sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 30.
Tuni dai shugaban ƙasar ta Indonisia ya katse wata ziyarar da yake yi a ƙetare domin sanya ido akan yadda ayyukan bayar da agaji ga mutanen da matsalar ta rutsa da su ke gudana.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu