1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afuwa ga 'yan luwaɗi a Malawi

Shugaban ƙasar Malawi ya yi wa wasu 'yan luwaɗi biyu da aka ɗaure afuwa

default

Shugaban Malawi Bingu wa Mutharika

Ratonnin da ke zuwa mana daga Malawi sun nunar da cewa shugaban wannan ƙasa yayi wa 'yan luwaɗin nan biyu da aka ɗaure afuwa. A lokacin da yake tarban Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon da ke rangadi a wannan ƙasa, Shugaba Bingu wa Mutharika ya ce ya bayar da izinin a sake 'yan luwaɗin biyu nan take. A makon da ya gabata ne wata kotun ƙasar ta Malawi ta yanke ma 'yan luwaɗin biyu hukuncin shekaru 14 a gidan yari bayan da ta samesu da laifin auratayya tsakanin maza tun watan Disemban bara. Sakataren MƊD wato Ban Ki-Moon na so yayi amfani da wannan ziyara ta sa wajen neman majalisar ƙasar ta Malawi da ta sassauta dokarta da ta shafi maza masu neman maza da kuma mata masu neman mata. Ɗaure 'yan luwaɗin da Malawi ta yi a makon da ya gabata ya jawo tofin Allah tsine daga sashen yammacin duniya ciki kuwa har da na Turai da kuma Amirka.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Mohammad Nasiru Awal