1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka G8 Jamus

Ahmad Tijani LawalJanuary 2, 2008

Jamus ta taka rawa wajen tallafawa Afurka a lokacin da take jagorancin G8

https://p.dw.com/p/CjRI
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: DW-TV

A haƙiƙa dai fadar shugabar gwamnati Angela Merkel ta sha yabo daga Bob Geldorf, mai sha’awar al’amuran Afurka a game da wannan rawa da Jamus ta taka a shugabancinta na gamayyar ƙasashen G8 dake da ci gaban masana’antu, inda ya ce ta taimaka aka kare makomar rayuwar miliyoyin jama’a a wannan nahiya. Duk kuwa wanda ya nazarci lamarin da idanun basira zai ga cewar Afurka ita ce ta fi ɗaukar hankalin mutane akan sauran batutuwan da Merkel ta ba da la’akari da su, kamar dai kare kewayen ɗan Adam lokacin shugabancinta ga ƙasashen G8. Angela Merkel ta fito fili ta bayyana cikakken goyan bayanta ga manufar taimaka wa Afurka domin ta samu bunƙasa tana mai yin kira ga ƙasashe masu ba da taimako da su aiwatar da alƙawurrrukan da suka yi a taronsu na Gleneagles su daina maganganu na fara baka kawai. Kazalika a ɗaya ɓangaren shugabar gwamnatin ta yi kira ga ƙasashen Afurka da su tashi haikan domin tsayawa kan ƙafafuwansu.

Merkel ta ce: Da farko dai a matsayinmu na ƙasashen G8 wajibi ne mu cika alƙawururrukan da muka yi. Amma a ɗaya ɓangaren muna sa ran ganin su ma ƙasashen Afurka sun yunƙura. A daura da haka ƙasashen na Afurka sun nema daga gare mu da mu yi bita mu ga ire-iren abubuwan da aka cimma da kuma inda aka gaza. Wannan shi ne abin da zamu mayar da hankali kansa lokacin taronmu a Japan nan gaba a wannan shekara. An yi tattaunawa mai armashi. Mun ankara da alhakin dake kanmu kuma zamu cika alƙawarin mu.”

Shugabar gwamnati Angela Merkel ta ƙara yawan taimakaon da tayi wa Afurka alƙawari a shekarar da ta wuce sannan ta kira taron ƙasashe masu ba da lamuni a birnin Berlin dangane da yaƙi da cuttuka kamarsu Aids da tarin fuka da zazzaɓin cizon sauro, inda ƙasashen suka yi alƙawarin taimako na dala miliyan dubu goma. A wannan shekarar da ta kama kuwa Jamus zata bunƙasa yawan kuɗaɗen taimakonta zuwa Euro miliyan 750, kuma Afurka ce zata samu rabo mafi tsoka. To sai dai kuma wannan taimakon ga Afurka ba tsakani da Allah ne kawai ba. Hakan na faruwa ne sakamakon katsalandan da ƙasashe irinsu China suka fara yi a wannan nahiya. A sakamakon haka shugabar gwamnatin ta Jamus take kira ga China da tayi koyi da ƙasashen yammaci wajen ƙarfafa manufar girmama haƙƙin ɗan-Adam a ma’amallarta da ƙasashen Afurka.

Merkel ta ce: Muna sane da cewar China ta duƙufa ka’in da na’in a nahiyar Afurka. Muna bin diddigin wannan lamari tare da taka tsantsan saboda sikankancewar da muka yi cewar duka-duka abin da Chinar ke kwaɗayi shi ne ɗanyyun kayayyaki, amma bata damu da makomar kewayen ɗan Adam ko shugabanci na gari a wannan nahiya ba.”