1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Kafofin Yada Labaran Jamus

November 18, 2004

Deutsche Welle da Cibiyar Nazarin Siyasa ta tarayya sun yi shirya wani taron kara wa juna ilimi na hadin guiwa domin bitar salon kafofin yada labaran Jamus a rahotannin da suke gabatarwa akan nahiyar Afurka

https://p.dw.com/p/BveV

Duk da dimbim kafofin dake akwai bila adadin wajen neman rahotanni da bayanai amma akasarin al’umar Jamus ba su da wata masaniya a game da yanayin rayuwar jama’a a kasashe 53 na nahiyar Afurka. Har yau wasu daga cikin Jamusawan suna dauke ne da salon tunani na zamanin mulkin mallaka a nahiyar Afurka. Kafofin yada labarai na kasar ba sa gabatar da wani cikakken bayani a game da yanayin rayuwar al’umar Afurka. Babban abin da kafofin yada labaran suka fi mayar da hankali kansa shi ne rahotanni na rikici ko yaki ko wata masifa daga Indallahi. A lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa game da haka wani dan wasan kwaikwayon Jamus dan usulin Senegal ya ce Afurka bata da wata kima a kafofin yada labaran kasar nan, in banda a bangaren masifu daga Indallahi, musamman idan lamarin ya rutsa da rayukan mutum sama da dubu dari. Amma bisa ga ra’ayin Michael Franzke, mai aike wa tashar telebijin ta Jamus ARD da rahotanni daga Afurka, babu wani banbanci tsakanin ‚yan jarida na Afurka da takwarorinsu Jamusawa wajen zabar rahotannin da suke yadawa, inda ya ce misali da zarar jirgin sama ya fadi, wannan rahoton ne zai mamaye kanun labarai, amma ba wanda ke batu a game da jiragen da suka tashi ko suka sauka salin-alin ba tare da wata tangarda ba. Banbancin dake akwai shi ne mutane a nan Jamus suna da cikakkiyar masaniya a game da zirga-zirgar jiragen kasa da shawagin jiragen sama, kuma aka fuskanci hatsari a wani lokacin. Amma a game da wani rahoto na ambaliyar ruwa ko faduwar jirgin sama ko hatsarin jirgin kasa a nahiyar Afurka sai a rika kallon lamarin ta wata fuska dabam. Su ma kungiyoyin taimakon jinkai na ba da la’akari sosai da sosai ga ire-iren wadannan rahotanni masu ta da tsikar jiki. Saboda a ganinsu duk wata masifar da zata samu, tamkar wata kafa ce ta janyo hankalin jama’a ga matsalolin nahiyar Afurka. Ulrich Post, kakakin kungiyar taimakon abinci ta Jamus ya ce hakan ya taimaka wajen jirkita hoton Afurka a idanun Jamusawa. Amma Lutz Warkalla daga jaridar Generalanzeiger ta Bonn yayi nuni da cewar, ainifin Jamusawan ba sa sha’awar al’amuran Afurka ne sosai, in banda rahotannin masifu daga Indallahi, bisa sabanin yadda lamarin yake a kasashen Faransa da Belgium inda ake da sha’awar jin labarai akan al’amuran nahiyar. Dukkan mahalarta taron na kara wa juna ilimi dai sun shiga saka ayar tambaya a game da yadda za a iya kawo sauyi ga lamarin, sannan ita kuma Anke Poenicke, kwararrar malamar tarbiyya ta ce wajibi ne a fara tun daga makarantu na faramar zuwa sakandare ta haka ne kawai za a iya canza salon tunanin Jamusawa a game da nahiyar Afurka.