1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Sharhunan Jaridu akan Afrurka

default

Jalisar Dokokin Kenya


Niger/Kenya/Zimbabwe

A wannan makon ko da yake jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne akan kasar Iraki dangane da kewayowar shekara ta biyar da gabatar da yaki kan wannan kasa da kifar da mulkin dan kama karya Saddam Hussein, amma duk da haka Jaridun ba su yi watsi da halin da ake ciki a kasashen Afurka ba, inda suka gabatar da sharhi da dama, misali akan kasar Zimbabwe. Amma da farko zamu fara ne da sharhin jaridar Die Tageszeitung akan matsalar tsadar rayuwa a nahiyar Afurka, inda ta ba da misali da kasar Burkina Faso tana mai cewar:

Niger

"Wani abin lura a game da tsadar rayuwar da ake fama da ita a nahiyar Afurka shi ne, mutane na kara durmuya cikin mawuyacin hali na talauci ne a duk lokacin da a daya bangaren wasu ke samun bunkasar arzikinsu. A yayinda a kasar China ake samun bunkasar yawan masu aiwatar da nama, a daya bangaren farashin burodi na dada yin tsada a nahiyar Afurka, sakamakon tsadar farashin alkama da shinkafa a kasuwannin duniya. Wannan matsalar ita ce ta iza keyar dubban dubatar mutane suka shiga zanga-zanga a kasar Burkina Faso, inda alkaluma suka nuna cewar a tsakanin watan janairun da ya wuce zuwa watan maris da muke ciki yanzu an samu hauhawar farashin kayan masarufi da misalin kashi 67%. Irin wannan mawuyacin hali kan kai ga adawa da gwamnati kamar yadda aka shaidar a makobciyar kasa ta Nijer shekaru uku da suka wuce."

Kenya

A cikin wani rahoton da ta gabatar a wannan makon kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Human Rights Watch tayi zargin cewar tun da farkon fari ne jami'an siyasar kasar Kenya suka shirya tashe-tashen hankulan da suka biyo-bayan zaben kasar da aka gudanar watan desamban da ya wuce, wanda a sakamakonsa mutane 1500 suka mutu sannan wasu dubu 600 kuma suka yi kaura, a yayinda a daya hannun tattalin arzikin kasar ya kusa ya tabarbare kwata-kwata. Jaridar Die Tagesspiegel tayi bitar lamarin ta kuma yi sharhi tana mai cewar:

"Wajibi ne a nemo masu alhakin wannan mummunar ta'asa a kuma gurfanar da su gaban kotu, kama daga bangaren 'yan hamayya na Raila Odinga da na gwamnatin Mwai Kibaki, wadda ta bai wa jami'an tsaro cikakkiyar dama ta bindige masu zanga-zanga a Kisumu da Nairobi, wadanda suka hada da mata da yara kanana da yawansu ya kai mutum 142. Dukkan sassan da lamarin ya shafa sun yi amfani ne da zama na dardar dake akwai tsakanin kabilun kasar ta Kenya domin rura wutar rikicin bisa manufar aiwatar da danyyen aikin nan da aka fi sani da suna wai tsaftace kabila."

Zimbabwe

Su ma al'umar kasar zimbabwe sun shiga fargaba a game da fuskantar wani mummunan hali irin shigen na kasar Kenya dangane da zaben kasar da za a gudanar mako mai zuwa. Jaridar Frankfurter Rundschau tayi sharhi akan haka tana mai cewar:

"Akwai alamun cewar zaben kasar Zimbabwe da za a gudanar mako mai zuwa zai banbanta da wadanda aka saba gani a kasar a zamanin baya sakamakon farin jinin da abokin takarar shugaba Mugabe, Simba Makoni ke da shi tsakanin jama'a, hatta a wuraren da a da shugaba Mugaben ke da rinjayen magoya-baya. To sai dai kuma abin fargaba shi ne ire-iren abubuwan da zasu biyo-bayan wannan zabe, wanda ko shakka babu ba za a kamanta adalci wajen gudanar da shi ba, lamarin da ya sanya manazarta al'amuran yau da kullum ke hasashen yiwuwar wani hali irin shigen na Kenya, duk da cewar kawo yanzu yakin neman zaben na tafiya salin alin ba tare da hargitsi ba."